RANDAR CIKIN ƊAKA...
©UMMU AFFAN
Page 7-8
Na kasa sauke magijin maganai na a kan ta, duk da ba sabon abu ba ne a gurina. Sallama nayi mata saboda sauke haƙƙinta da ko ita ba na jin zan yi. Ganin na doshi hanyar ɗakina gadan-gadan ta kuma tuntsirewa da dariya tare da rangaɗa buɗa da buga cinya.
"Ahayye nanaye, wa ya ga suɓul da baka, har an dawo kenan!" Ta kuma saka dariya har da riƙe ciki, sai yanzu na fahimci dariyar da take mini. Ganin na fita cikin farinciki sai ga shi na dawo a burkice, ba ma wannan ba naje gidanmu amma ban yi cikakkiyar awa biyu ba na dawo. Sanin ta san komi ya sa na shige ɗakina ban kulata ba.
Toilet na shiga nazo na gabatar da sallar azahar da aka idar yanzu, na miƙe da ƙyar na shiga kitchen ba don son ina san cin abinci ba, sai don lafiyata, idan ban ci ba nasan zai zame mini matsala babba. Girki na dafa taliya guda ɗaya da taji haɗi na musamman na saka green beas. Ina kammalawa na zuba nawa a plate na bar sauran tukunys, nasan acicin can idan zan kwana gida ba zata yi girki ba har sai na dawo na dafa zata ci. Ina shiga ɗaki na zauna tare da bisimilla na fara cin abincin. Turawa kawai nake saboda yunwa amma ba domin daɗin shi ba, don bakina sam babu tastin.
Ƙarar wayata yasa naji hantar cikina ta motsa musamman da naga baƙuwar lamba.
"Hello!"
Na furta bayan ɗaukar kiran.
"Ranki ya daɗe!"
Ƙirjina ya ba da wani sauti mai ƙarfi.
"Adyaan?"
Na tambaya duk da na gane muryarsa ce.
"Ƙwarai shi ne, fatan na barki lafiya. Wallahi Nihlah na kasa samun natsuwa ne shi ya sa na kira domin naji muryarki."
Sautin bugun ƙirjina ya ƙara tsananta sauti.
"Ka manta ni batar wani ce?"
"Matar Mudassir ko na ce Mrs Md ina sane."
Ajiyar numfashi na sauke.
"Ka ga kenan wannan furucin bai dace da ni ba."
"Nihlah ki saurare ni, duk halin da kike ciki a gidanki nasan komi. Don haka ina mai baki shawarar ki ruguza wannan auren naki da babu cancanta kizo mu fuskanci gabanmu."
"Ya isa..!"
Na daka mi shi tsawar da ban san zan iya ƙarar sautin a lokacin ba, kasantuwar halin da nake ciki.
"Kar ka sake kirana daga yau ina mai umartarka."
"Bazan iya ba, amma ina mai baki haƙuri idan ranki ya ɓaci."
Ƙit na katse kiran tare da ture abincin gabana, hawaye na zubar mini, nan take kuma naji wani mugun sanyi na shigs sassan jikina. Curewa nayi guri guda ina sauke numfashin wahala, naji alamar masassara (Zazzaɓi) ce ke niyar kayar da ni. A hankali na gangara wato na sulale a ƙasa tare da jawo bargon dake gefen gadona na lulluɓe duka jikina ina rawar ɗari (Sanyi).
Na daɗe a cikin wannan yanayin ba mai taimako sai Allah, domin idan mutuwa zan yi sai na mutu Amal ba ta sani ba, domin ba shugowa ɗakina take ba sai da dalili mai ƙarfi.
Inaji ana kiran sallar la'asar amma na kasa ko da motsawa daga inda nake, duk na cure guri guda haƙorana har haɗewa suke da juna.
Misalin ƙarfe biyar Yaya ya shugo, nasan lokacin ne yake dawowa gida, sallama ɗauke a bakin sa ya shugo. Bai ankara ba yayi ƙwallo da plate ɗin da naci abinci, a hankali na zame zanin daga fuska daidai sakin tsakin shi.
"Wulaƙanci ƙazantar da ki ka koma kenan, kici abinci ki bar kwano a gurin?"
Kallon shi kawai da jajayen idanuwana da suka rine sakamakon ciwon da na shiga,
"Kayi haƙuri Yaya!"
Ina tunanin yadda yaji muryata ne ya sa shi kallona da sauri. Ɗakin ya kalla sannan ya kuma duba na.
"Lafiya kuwa?"
Ya tambaye ni, hawayen da nake son dannewa suka gangaro.
"Yaya tunda na dawo masassara ta rufe ni."
"Allah ya baki lafiya!"
Ya furta sai naga ya fita, kusan minti ashirin har na fidda rai da dawowarsa sai gashi ɗauke da ledar magani da alama a chemis ya saya mini.
Ajiyewa ya yi, kusan minti biyar da fitarshi ya dawo hannunsa ɗauke da kofi, umarni ya ba ni a kan na ta shi. Hawaye na matso, "Bazan iya ba Yaya." Ɗan tsaki yaja kafin yasa hannun sa ya ɗago ni, bakin gado ya ajiye ni tare da miƙa mini kofin, da sai da ya miƙo na gane tea ne ya haɗo mini, ya sha madara kam.
"Baza ki sha kafin na gama."
Kakkaɓe ɗakin ya fara tare da ɗauke plate ɗin ɗazu ya kai kitchen sannan ya dawo ya share ɗakin fes. Har zuwa lokacin ina ta kallon shayin amma na kasa sha, sai da ya gama ya dawo, wani kallo ya mini da yasa nayi saurin kai kofin bakina, runtse ido nayi ina kurɓa a hankali, har na sha kusan rabi. Ganin ina niyyar amai ne ya amsa tare da miƙo mini pure water ya bani magungunan kusan kala biyar, tuni na fara kuka don ba abin da na tsana irin magani, har gara a mini allura akan nasha magani. Kallon da yake mini yasa na runtse idanuwana da ƙarfi nasha, amai nake ji amma dole na mayar da shi gudun hukuncin Yaya, lallaɓa nayi na ɗauro alwala nazo nayi sallar la'asar da ban yi ba a zaune, a wurin na sulale bacci ya yi awon gaba da ni.
Amal pov.
"Maganar gaskiya Nihlah ta iya girki, Allah ya wadataka da matar da ta iya girki ka more."
Yaya Mz ya faɗa yana kai lomar taliyar da Nihlah ta dafa ɗazu, wacce Amal ta ɗumama musu yanzu.
Ɗaure fuska tayi sosai tana hura hanci, tare da cewa,
"Na ma ƙoshi!"
"Wallahi ta ƙara auki daman ina jin wannan kamar ba za ta ishe ni ba."
Ya jawo plate ɗin Amal idan yaci nata yaci na shi kuma bai daina santin ba.
"Maganar gaskiya Yaya ka ishe ni, haba don Allah ko ance maka ni ban iya ba ne?"
Murmushi ya yi, "A'a ko ɗaya, ai kinga yau sai ki mana na dare."
Murmushi ta saki tare da cewa "Ƙwarai kuwa zaka ci girki mai daɗi yau."
Bai tanka mata ba, har ya kammala yasha ruwa sannan ya miƙe ya ce mata ya koma kasuwa.
Sosai Amal tayi mamakin rashin fitowar Nihlah, sai tayi tunanin tasan da taje gida ba a mata ta daɗi ba, wataƙil damuwar hakan ce ta hanata fitowa. Dariya ta kuma yi a fili ta ce,
"Ke ba ga 'yar daɗi miji ba, an fita ana wani iya yi wai Yaya zai sauke ni a gida, ai kin ga ƙarshen tika-tiki tak!" Ta kuma sakin dariya. Biyar nayi ta shiga kitchen ta daddage wai tanawa miji girki. Shinkafa da waƙe ta da faduka tayi, wacce bata ankare ba ta mata ciki biyu wato gefe ɗaya ya dahu ɗaya bai dahu ba kuma ta chaɓe, ruwa ta fara ɗaurawa sai da ya dahu luguf sannan ta zuba shinkafa a sama, da ta kusa dahuwa ta saka maggi gishiri ta markaɗa kayan miya ta saka sannan ta sa mai. (Jagwalgwalo lolx) babu wasu kayan ƙamshi da na armashi, kuma sai murna take ta kammala girki. Fitarta kitchen ke da wuya, Yaya Md ya shugo, bin ko ina yayi da kallo duk kitchen ɗin a hargitse duk abin da ta ɓata a gurin ta barshi, ƙasan duk ya ɓaci. Ƙaramar tukunya ya ɗauka ya ɗauraye sannan yasa ka ruwa kofi ɗaya da lipton da yayi zafi ya saka suger madara da milo ya fito yana jan tsaki yaƙi jinin ƙazanta.
Amal kuwa wanka ta shiga ta tsantsara gayu sannan tazo ta shirya mishi abinci a kula, sauran ta bari a tukunya. Ta so ta fara ci sbd yunwar da take ji amma zuciyarta ta bata haƙuri ta bari har Yaya Mz ɗin ya dawo, domin ya fara ci don tasan sai yaci plate biyu, sannan ita ma tasan biyu sai ta cinye don Allah yayi ta da mugunci, Shiyasa bata tsallake kwana ɗaya bata yi bayan gida ba (Kashi lolx)
Misalin takwas da rabi na dare suke zaune suna haramar cin babbar gara. Amal sai murmushi take ta ce,
"Daga yau dai sai na fita daga bakin duniya, kuma a daina yabawa wata a gabana, kana da miji yana yabon wata."
Babu abin da Yaya Mz ke yi sai dubanta, duba na tsanake. Kafin ya mayar da hankali akan abincin da ko a ido bai yi ƙyan gani ba, bai musa mata ba don kar ya kashe mata guiwa ya jawo abincin. Lomar farko da ya kai ya yi saurin furzarwa, da sauri ya ɗauki ruwa kuskure bakin sa ya yi sannan yasha ruwan.
"Lallai sai yau na ƙara tabbatarwa baki da hankaki, wannan haukan naki ne abinci? To maza ki cinyeshi don bazaki mini asarar banza ba, yanzu neman kuɗi da wahala, gargaɗi da murya mai ƙarfi kar ki kuma caɓa mini abinci haka."
Tunda ya fara maganar ta fara hawayen, ta dage tayi girki amma yana kushe mata. (Kuskuren ƙin koyawa yaro girki da aiki tun yana gida, sai ake gani kamar hakan gata ne, ana bawa wani can da sunan cuta to wanda ake ba taimakonsa ake wallahi. Tunda zai shigs gidan aurensa ya iya komi. Hattara iyayen zamani.)
A fusace ya bar gurin, jawo abincin tayi da niyyar ci, sai dai tana loma ɗaya ta raya a zuciyarta doke ya yi fushi don ko kasheta za a yi ita ma bazata iya ci ba. Kwashe komi tayi ta mayar kitchen sannan ta dawo parlourn wayarta ta ɗauka ta kira Ummanta, tana ɗauka ta fashe mata da kuka.
"Shalele lafiya ki ke kuka, me ya faru?"
Cikin kuka ta ce,
"Umma komi nayi a gidan nan ban iya ba, Yaya Mz ya yi ta yabon girkin Nihlah yau dai na daure nayi mishi wallahi kamar zai dake ni girkin bai yi daɗi ba."
"Kwantar da hankalinki shalelena, yau kin kwaɓa gobe da safe ki farka da wuri ki girka mi shi abin kari mai daɗi. Ni kaina ba na so ana yabon wannan maiyar Allah yasa ba kurwa ta kama mi shi ba."
"Wallahi komi nayi ban iya ba sai ita munafukar, amma da safen zai sha mamaki Umma."
"Yawwa 'yar lelena kiyi mai daɗi fa."
"To Umma!"
Sallama suka yi, sannan ta koma ɗaki. Tarar da shi tayi yana cin biredi da jus. Zaunawa tayi kusa da shi ya daka mata tsawa, ba shiri ta tashi tana harararshi.
Ta kwanta da niyyar zai sha mamaki domin girki na musamman ta shirya yi mi shi.
Yaya Muzammil (Mz) kuwa ranar yaci wahala saboda ya saba da daddaɗan girkin Nihlah yau kuma babu, shi kuma ma'abocin kwasar girki ne bai wasa da cikin sa. Da tunanin Nihlah ya kwanta, me yasa yau bata musu girki ba, anya ma tana lafiya kuwa? Da saƙe-saƙen nan bacci ya yi gaba da shi, sai asuba ya tashi, toilet ya faɗa ya ɗaura alwala ya wuce masallaci. Da zai shugo gida wajen shidda da rabi suka haɗu da Md da alamar ba gidan ya kwana ba, gaisawa suka yi.
Ya ce"Na kwanta ina ta tunanin halin da Nihlah ta kwana, wunin jiya duk bata da lafiya."
"Subuhanallah! Ai ban sani ba, kuma ina tunanin Amal ta sani kuwa ba ta faɗa mini ba."
Md bai ce komi ba ya yi gaba, Mz na biye da shi har cikin ɗakin. Yanzu ma cikin ba daɗi don haka ta kwana da zazzaɓin, sai sannu Yaya Mz ke zuba mata, Yaya Md ya ce,
"Bari na haɗo mata tea tasha sai tasha magani."
Da sauri Mz ya miƙe. "Bari na haɗo mata." Da sauri ya fita, bin kitchen ɗin ya yi da kallo a zuciyar sa yana yabawa Nihlah yasan da lafiyarta ƙalau ba zata bar shi haka ba, amma waccen ballagazar sai a hankali.
Bayan ya kai mata da ƙyar ta iya sha sannan tasha magani. Sannu Mz ya kuma mata ya fita saboda yau da wuri zai fita, bai yi minti goma da fita ba shima Yaya Md ya yi tafiyarsa.
Ko da ya koma ɗaki bata farka ba, tsaki yaja ya shirya tare da mata rubutu a takarda ya yi ficewar shi.....
08104335144
Masu buƙatar littafin za suyi magana ta lambar da ke sama ko a tura kuɗi kai tsaye 500 ta 8104335144 Opay wallet Fatima Rabiu Sunusi sai a tura shaidar biya ta 08104335144 na gode.
#Nihlatulkhair
#YahMd
#YahMz
#Adyaan
#Amal
#Farrah
#UmmuAffan
#RandarCikinƊakaa