Tsantsar Ƙauna – Kashi na 3
Wallafar Tahir Yusuf (Novels Elite)
Bayan karanta saƙon Kamal, Fatima ta zauna kan gadon dake ɗakinta, zuciyarta cike da damuwa. Tana jin kamar rayuwarta na gab da rugujewa. Auren da ba ta so yana gab da faruwa, amma masoyin zuciyarta yana yi mata nuni da ta tashi tsaye.
Da sassafe, ta zauna da mahaifiyarta Hajiya Rabi. Da hawaye a idonta, ta ce: “Mama, wallahi bana son Suleiman. Na riga na samu wanda nake so tun kafin a fara batun aurensa.”
Hajiya Rabi ta kalle ta da mamaki: “Ke Fatima? ashe baki da hankali, menene laifin Suleiman? Baban ki ne ya yanke hukunci, kuma ba za ki kunyatar da shi ba!”
Fatima ta fita daga gida da kuka, ta nufi gidan su Kamal. Bai da labarin zata zo. Da ya gan ta a tsakar gidan su, ya tsaya cak. Idonta ja, da ka ganta kasan taci kuka har ta godema Allah.
Ta ce da shi: “Kamal… ina son ka so tsakani da Allah, cikin sheshsheƙar kuka Fatima ke fadin " Kamal kada ka bari na Auri wanda Zuciyata bata so, Zuciyata naka ne kai kadai, da kai ta saba" cikin damuwa ya ƙara kallon Fatima tare da fadin, Fatima Nima ina son ki, amma lamari na iyaye a hankali ake bin shi, ki bar komai a wajena, zan je gidan ku nayi magana da su Bana.
Ranar Lahadi, Kamal ya je gidan su Fatima, sanye da kaya masu tsabta shiga irin na mutane masu kamala, zuciyarsa cike da tsoro. Ya gabatar da kansa gaban Malam Abubakar, mahaifin Fatima, yana fadin: “Ni ne Kamal, dan makwabtanku. Ina son 'yar ku Fatima, kuma ina neman izinin neman auren ta.”
Ɗakin ya ɗauki shiru kamar babu rai. Malam Abubakar ya zaro ido, ya ce: “Kamal? Kai? Da tunanin ka zaka iya wuce Suleiman da ya dawo daga China”
Cikin natsuwa Kamal ya ce: “Ina da ilimi, ina da sana’a, kuma ina ina son Fatima da gaske. Duk da ba ni da kudi kamar Suleiman, ina da zuciyar da zata girmama ‘yar ku fiye da dukiya.”
Fatima ta shigo ta zauna kusa da Malam Abubakar, cikin Muryar tausayi. Ta ce: “Abba, dan Allah… ni Kamal nake so, dan Allah kada ku raba Ni dashi.”
Hajiya Rabi ta taso da fushi, amma Malam Abubakar ya daga hannu ya dakatar da ita. Ya kalli Fatima, sai ya ce: “Fatima kece 'yata mace, bazan aura Miki wacce baki so ba, ki je kiyi addu'a kawai” nan Fatima da Hajiya Rabi suka fice daga falon.
Kamal kuwa kan sa na ƙasa zuciyarsa na ta sake-saƙe har Malam Abubakar yayi magana bai ji ba, sai da ya taɓa shi, nan Mal. Abubakar ya amince da Soyayyar Kamal da Fatima.
A wannan rana, an janye batun auren Suleiman. Kamal da Fatima suka zauna a zauren gida kamar waɗanda aka sauke musu dutse daga kai. Iyayen Kamal sun shiga cikin lamarin, suka ɗauki nauyin daurin aure a makon gobe.
Naku a koda yaushe Novels Elite
Wannan shi ne ƙashi na uku, mai cike da soyayya, gwagwarmaya da nasara.
Shin wannan labarin ya burge ku, idan ya burge ku kuyi sharing.