Tsantsar Ƙauna – Kashi na huɗu
Tun bayan amincewar iyayen su Kamal, gidan su Kamal da gidan su Fatima suka kama shirye-shiryen ɗaura aure. Ana ta ɗinki, ana sayayya, ana shirin liyafa. Farin ciki ya lullube duka iyalai, kamar aljanna ta sauka cikin ƙofar gidan.
Kamal kuwa, yana ta saƙa mafarkin rayuwa da Fatima yadda za su zauna cikin zaman lafiya da soyayya, yadda za su gina rayuwar su akan tsari, yadda za su raini yara cikin ƙauna da tarbiyya. Kamar komai ya cika.
Amma kwana goma kafin ɗaurin aure, wani abu ya faru da ya razana kowa. Da yamma, Fatima na dawowa daga kasuwa, sai ga Suleiman – wancan saurayin da aka so a aura mata da farko – ya tare ta a kan hanya.
Ya kalleta da idanu masu cike da ƙiyayya, ya ce: “Kin raina ni Fatima. Amma wallahi kin jefa kanki cikin matsala. Ni ba zan bari wani ɗan talaka ya dauke min ke haka ba zanyi duk abinda zan iya don na hana wannan aure, duk abinda na rasa kowa ma sai ya rasa.”
Cikin tsoro da fargaba Fatima ta matsa gefe jikin ta na karkarwa, ta ce: “Don Allah Suleiman, ka rabu da ni. Ka yarda da kaddara. Ka nemi wacce zata so ka da gaske.
Da dare misalin ƙarfe 8:30 Kamal na zaune cikin ɗaki yana latsa wayar sa, sai wani sako ya shigo wayar sa na ban tsoro. Barazana ce: “Ka bar Fatima domin kuwa ita ɗin yawa ce Ni ƙadai, ko kuma zaka fuskanci abinda ba ka taɓa zato ba.” Kamal ya karanta wannan saƙon cikin natsuwa, sai ya ya fita daga cikin saƙon ya cigaba da abinda yake yi..
Da safe, ya je gidan su Fatima ya gayawa Alhaji Abubakar duk abinda ke faruwa. Alhaji ya buga kujerarsa da hannu, yana cewa: “Wannan wauta ce! Ba za mu tsaya ba! Duk wanda yake son lalata farin cikinmu, zai ci amanar kansa.”
Zan tsaya tsayin daka. Ni ba zan ja da baya ba. Kuma ko da me zai faru, ba zan bar Fatima ba.” Kamal ne ke faɗin hakan a cikin Zuciyarsa, Malam Abubakar ya ce da Kamal kaje abin ka in sha Allah ba abinda zai faru.
A ɓagaren Hajiya Rabi kuwa zama tayi da Fatima a ɗaki. Ta ce: “Fatima, da na fara goyon bayan Suleiman a baya da zaton cewa shi mutumin kirki ne, yau na gane gaskiya. Kamal ne mutumin kirki. Kar ki bari wani ya tsoratar da ke, ki natsu ki tsayar da zuciyar ki waje guda kuma ki dage da addu'a”
Fatima wacce take zaune kamar wacce ake zare ma lakkar jiki ta ji wani karfi ya dawo jikin ta da ƙwari. Soyayyarta ga Kamal ta ƙara girma – ba domin kawai yana sonta ba, amma don yadda yake tsayawa akan gaskiya da mutunta manya.
Ranar Asabar, da safe, Kamal da wasu abokansa suka kai rahoto ofis din 'yan sanda dangane da barazanar saƙon da Suleiman ya tura masa. An ɗauki mataki, an kara tsaro a unguwa, domin tabbatar da komai ya tafi lafiya.
Bayan jin haka, zuciyar Fatima ta ƙara kusantuwa da Kamal. Duk lokacin da suke tare, tana jin tamkar duniya ta tsaya ce ta tsaya mata, hakan yasa ko yaushe soyayyar Kamal ke ƙaruwa a cikin Zuciyarsa.
A daren Alhamis, kwana biyu kafin auren, Kamal ya kira Fatima a waya. Ya ce da ita da murya mai taushi: “Fatima, zan rayu da ke cikin ko wani hali,. Ke ce hasken rayuwata. Ki yi min alƙawari cewa za ki kasance tare dani har ƙarshen rayuwar ki.”
Fatima ta amsa da murya mai sanyi: “Kamal, ka fi dukiya, ka fi duk muryoyi masu ƙarya. Kai kaɗai ne cikin Zuciyata, kai kaɗai ne zan iya rayuwa ta kai har abada.”
Dare ya yi sosai basu sani ba suna waya, kuma zuciyoyin su biyu na bugawa da irin soyayyar da ba a iya fassara ta da baki. Wannan ba soyayya ce ta wasa ba. Wannan ita ce Tsantsar Ƙauna, ƙaunar da ake sadaukar da kai saboda ita.
Don jin ya zata kasance mu haɗu a kashi na biyar.
Kada a manta ayi mana comment da Sharing sannan ayi liking ta haka ne zamu gane kuma jin daɗin wannan littafin.