Tsantsar Ƙauna – Kashi na Shida
Na
Tahir Yusuf (Novels Elite)
Kamal ya ɗan juyo yana kallon fuskarta da idanun sa masu cike da tausayawa. Wata ƙaramar iska ta buso sakamakon fansar dake juyawa, tana kaɗa fuskart , Ya ɗan lankwashe hannunsa, kamar yana so ya kama nata, amma sai ya tsaya. Bai ce komai ba, amma idonsa na faɗin abubuwa masu yawa.
“Fatima,” ya ce a hankali. “Ina son a ce shekara biyar masu zuwa, muna zaune tare, muna kallon yara suna wasa a cikin gida. Ina son a ce muna tuna wannan dare.”
Fatima ta lumshe ido tana ɗan murmushi tare da jin daɗi a Zuciyarta da jin kalamansa. Ta ce, “Ni kuwa ina mafarkin lokacin da zan ce da kai ‘zan fi kowa farin cikin ganin wannan lokaci
Suka yi dariya tare. Amma wannan dariyar ba ta da sauti mai yawa – dariya ce ta jin daɗi mai zurfi, ta fahimtar juna.
Bayan ɗan lokaci, Kamal ya miƙe yana gyara hularsa. “Zan tafi yanzu,” ya ce, “amma kafin nan, zan tambaye ki abu guda. Fatima, kina min alkawari?”
Fatima ta ɗago kai, ta ce: “Na riga na yi alkawarin zuciya. Amma gaya min, wane ne naka?”
Kamal ya ce: “Kada ki bari kowa ya karya miki zuciya, ko da kuwa ni ne. Idan na taɓa yin wani abu da zai ɓata miki rai, ki tuna da wannan dare.”
Fatima ta ce cikin tausayi: “Kamal, ina ganin zuciyarka. Kuma ina jin ƙamshinta. Ba zan yarda wani ya bata min labarin da na riga na fara rubutawa ba.”
Sun yi shiru na ɗan lokaci. A can gefe, wata ƙaramar yarinya ta wuce tana rera waka cikin muryarta mai sanyi. Wakarta ta cika falon, kamar fassarar da zuciyoyin su ke yi ba tare da su faɗi komai ba.
Sai Kamal ya ce: “Yakamata mu fara maganar aure"
Fatima wanda farin ciki ya cika mata zuciya Tayi murmushi tace " gaskiya haka ya kamata "
Da haka suka rabu da dare, kowannensu ya tafi da sabon fata, sabon hangen nesa Soyayyarsu ta ƙara ɗaukaka, ta shiga sabon mataki matakin gaskiya, da niyya, da amincewa.
Nan zamu tsaya a kashi na shida sai mun haɗu a kashi na bakwai, ayi haƙuri ina posting kaɗan saboda Ni dan koyo ne bana so na cika da yawa