Tsantsar Ƙauna kashi na biyar

Tsantsar Ƙauna Novels

 Tsantsar Ƙauna – Kashi na Biyar

 

Na 

Tahir Yusuf (Novels Elite)


Washegari da safe, Kamal ya tashi da murmushi a fuska. Bai manta da kalaman Fatima ba, sun kasance kamar furanni a zuciyarsa, suna waro ƙamshi a kowace numfashi da yake yi. Yana zaune a daki yana kallin hotunan shirin aure a kafar sada zumunta na facebook, yana murmushi shi kaɗai.

A bangaren Fatima, ita ma rayuwarta ta sauya. Tun daga lokacin da ta furta “Zan rayuwa da kai har abada”, zuciyarta ta samu natsuwa. Ta san wannan soyayyar tana da tsabta sannan tana da daraja. A yau ta zauna tana rubuta ma Kamal text wato sakon ko ta kwana (sms) na soyayya kamar haka; "Assalamu alaikum, Farin cikin Rayuwata, Uban 'Ya'Ya na , da fatan ka tashi lafiya." Cikin abinda bai wuce minti ɗaya ba Kamal ya Turo mata nsahi sakon kamar haka; "wa'alakumussalam, na tashi lafiya, Ke ce mafi kyawun abu da ya taɓa faruwa da ni. Ina son ki fiye da komai a duniya" farin ciki ya cika zuciyar Fatima, tana furta "ina son Kamal" ba tare da sanin maganar ta na fita ba. Hajiya Rabi dake tsaye mamaki ne ya cika ta. Ta kalle tana faɗin "Allah ya shirya ki" ta fice daga ɗakin. Abinda da wanda ke cikin shauƙin soyayya kamar ba da ita ake magana ba. Kiran Kamal ne ya shigo wayar Fatima batayi wata-wata ba ta ɗauka tare da karawa a kunne ta, cikin sassanyar murya mai kashe jiki, Fatima ta amsa wayar Kamal da cewa,

"Kamal, Rayuwa ba ta da ma'ana face da kai. Duk lokacin da nake tare da kai, ina jin zan iya fuskantar duniya. Kamar rana ce ka shigo cikin dare na. Na ji daɗin yadda kake sona ba tare da sharadi ba, ni taka ce har tsawon rayuwa ta" da haka dai sukayi ta waya har zuwa ƙarfe 11:00 na safe suka rabu, kowa ya cigaba da ayyukan dake gabansa.


Da yamma, Kamal ya zo gidan su Fatima kashin  turare ne ke tashi a cikinsa kai kace cikin shafin turaren kake, bayan Fatima ta fito. Ya kalle ta cikin natsuwa " Fatima rufe idon ki ki miƙo min hannun ki" da sauri tayi yadda ya umurce ta domin yasan bazai cutar da ita ba, Wani abu taki ya saka mata a hannu sannan ya saka mata wani leda a dayan hannun nata, " to bude idon ki."

Wani irin zobe ne azurfa ne amma anyi masa kwalliya da zinare da wani irin dutse a sama shi, Fatima wacce ke tsaye baki ta bude wanda kana ganin fararen hakorarta. "Mama ce tace na kawo Miki, wannan ledar kuma kaya ne a ciki wanda Mama da kanta ta zaba Miki su".

Ban san da wani irin kalamai zan gode maka ba, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya ƙare min kai a duk inda kake" har yamma tayi sosai gab da Magriba sukayi Sallama Fatima ta shiga gida..


Bayan sallar Isha, Kamal ya dawo wajen Fatima inda cikin gidan ya shiga ya zauna cikin falon Baban su Fatima sakamakon baya nan Kamal kuma ya zama tamkar ɗan gida. Kamshin turaren da Fatima ta saka ne ya fara sallama cikin falon kafin siririyar Muryar Fatima ya shigo, Kamal kasa rufe baki yayi ganin irin shigar da Fatima tayi. Dinkin atamfa ne riga da Skirt ruwan doka babu hijabi ko mayafi, wanda suka zauna daidai a jikin Fatima gata ba fara sosai ba kuma ba zaka ce mata baƙa ba. Ta katse tunaninsa ta Baban 'ya'yana. 

Kamal ya kalle ta ya ce: “Kin san me nake ji Fatima?”


Ta ce, “A’a. Sai ka gaya min.”


Ya ce: “Ina jin kamar yau ne na fara rayuwa. Kuma ke ce farkon shafin.”


Fatima ta yi shiru, tana kallon TV din dake falon. Ta ce: “To mu rubuta labari mai kyau. Labarin da ba zai taba shuɗewa ba, kamar yadda ƙaunarmu ba za ta gushe ba.”

Mu haɗu a kashi na shida don jin wani irin labari zasu rubuta.

Post a Comment

Previous Post Next Post