Tsantsar Ƙauna – Kashi na 1
Na
Tahir Yusuf (Novels Elite)
A Unguwar Layin Liman, cikin garin Zariya, Kamal da Fatima sun taso tare layin su ɗaya gidan na kusa da juna, Iyayensu suna da alaƙa ta zumunci, su na yawan ziyartar juna, har hakan ya sa yaran biyu suka saba da juna kamar ‘yan uwa.
Tun suna yara, Kamal ya kasance mai natsuwa, yayin da Fatima kuma tana da yawan fara’a gata kyakkyawa hakan yasa kowa nason kula ta. Mafi yawan lokuta duk inda Kamal ya je, tare suke tafiya da Fatima.
Lokacin da suka kai shekara goma sha biyar, sun fara fahimtar cewa abinda ke tsakaninsu ya wuce kawai abota ko makwabtaka. Kamal ya fi jin daɗin zama da Fatima fiye da duk wata yarinya a unguwar, haka ita ma Fatima tana jin wani abu daban idan har Kamal na kusa da ita.
Amma su ba su taɓa fadar hakan ba. Rayuwa ta ci gaba, makaranta ta shiga tsakani, kuma zamansu ya ɗan ja baya. Kamal ya tafi Federal Government College, Malali Kaduna, sakamakon Scholarship da ya samu yayinda ita kuma Fatima ta tsaya a Zariya tana karatu a GGSS Tudun Wada.
Duk lokacin hutu, Kamal na dawowa gida, suna gaisawa da dariya amma zuciyarsu na ɓoye kalmomi masu nauyi: "Ina sonki" da "Ka fi kowa a raina". Sai dai kowanne na tsoron karya abota da ke tsakaninsu.
Wannan shi ne farkon labarin “Tsantsar Ƙauna”
Mu haɗu a shafi na biyu.