Tsantsar Ƙauna Page 2 - Abokiyar Hira Novels

Tsantsar Ƙauna Novels
Tsantsar Ƙauna – Kashi na 2


Na 

Tahir Yusuf (Novels Elite)


 Ranar Sallah Babba ce, rana ce da yara da matasa har ma da manya suna yin yawo da sabbin kaya, farin ciki a ko’ina. Kamal ya dawo daga Kaduna don hutu. A lokacin da ya sauka daga babur ɗin haya a gaban gidansu, sai ga Fatima ta fito da bokiti a hannu.

Sun haɗa ido da Fatima, kamar yadda suka saba baya, amma akwai sabon abu a cikin kallon Zuciyarsu ta bugawa da sauri kai ka ce sun yi gudu ne,  suka gaisa da sanyi, amma ba wanda ya ce komai fiye da: “Barka da zuwa.”

Da dare, Kamal ya leƙa gidansu Fatima don kai gaisuwa. An sha fura da kosai, an yi dariya, amma shi da Fatima sai dai wannan ya kalli wannan da ke fassara soyayya fiye da kalmomi.

Bayan ‘yan kwanaki, Kamal ya gayyace ta zuwa tafiya zuwa dutsen Samaru da wasu abokansa. A lokacin tafiyar, Kamal ya tsaya gefe da ita, Sai ya ce: “Fatima… kina tunawa lokacin da muke yara?”

 Ta ce: “Ai ban taɓa mantawa ba. Ka kasance aboki na mafi kusa.” Daga nan sai su kayi shiru na ɗan wani lokaci. Kamal ya cigaba da cewa: “Har yanzu kina min kamar da?”

6Ta kallii ƙasa, tana wasa da yatsanta, cikin sanyin Murya sanyi tace: “Kamal… ba kamar da ba. Yanzu sai dai… na fi sonka fiye da kowane mutum.”

Kamal ya yi shiru na dan lokaci, ba don bai so ba, amma don zuciyarsa na bugawa da sauri kamar za ta fito. Daga nan ya ce: “Fatima, kin fi kowa muhimmanci a rayuwata. Tun muna yara, har yanzu zuciyata na tare da ke.”

Daga wannan rana, komai ya canza. Sun fara fahimtar cewa zuciyarsu biyu suna fitar da sauti iri ɗaya, sautin ƙauna ta gaskiya.

Amma kamar kowanne labarin soyayya, ba komai ke tafiya da sauƙi ba. Cikin sati biyu, wani baƙo ya shigo cikin labarin Soyayyar Fatima da Kamal, Suleiman, ɗan abokin mahaifin Fatima, da aka kawo don a ɗaura aurensa da ita nan da wata biyu.

Fatima ta rikice. Babu wanda ya tambaye ta ra’ayinta, kuma babu wanda ya san cewa zuciyarta ta riga ta kulle da sunan Kamal. A gidansu, an riga an amince da Suleiman saboda shi ɗan kasuwa ne mai kudi.

Ranar da Kamal ya samu labari, sai zuciyarsa ta ji kamar an huda ta da wuƙa. Yayi shiru, bai fada mata komai ba, amma kwana bakwai bai leƙa gidansu Fatima ba  zuciyarsa cike da ƙiyayya da raɗaɗi.

Fatima kuwa ta kasa sukuni. Ta aika sakon rubutu da cewa: “Kamal, kada ka yi shiru. Ni ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba.”

Kamal ya dawo da amsa: “Idan da gaske kina so na… ki tsaya ki fuskanci iyayanki. Wannan ba lokaci ba ne na shiru, Fatima. Wannan lokaci ne na yanke hukunci.”

Shin Fatima zaka iya faɗa ma iyayenta soyayyar su da Kamal ko kuma za tayi shiru Mafarkinta ya rushe?

Mu haɗu a kashi na uku

Post a Comment

Previous Post Next Post